BANBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA

*BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA* *Tambaya :* Assalamu alaikum malam.Don Allah ina da tambaya: wai ma ye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya saida akan nera 8 ? *Amsa :* wa alaikum assalam, To malama riba ta kasu kashi biyu : 1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren. 2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu. Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka. Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so idan mutum yana siyar da kaya ya saukaka, Annabi s.a.w. yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame", kamar yadda ya zo a hadisin Bhukari mai lamba ta : 2076 Allah shi ne mafi sani *Amsawa*✍🏻 *DR.JAMILI YUSUF ZAREWA* 23/4/2013

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 939 · February 23, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853