NAYI SAHU JERE DA LIMAN, YAYA SALLAH TA?

*_NAYI SAHU JERE DA LIMAN, YAYA SALLAH TA?_* *Tambaya* Assalamu alaikum warahmatullah. Allah ya karbi ayyukan alkhairan da Mallam yake gudanar wa a matsayin ibadah, amin. Tambaya ta anan itace, mutum da yaxo ya samu Sahun sallah ya cika, sai ya je ya jera da Liman a gaban Sahun. Shin hakan ya dace? Ina neman Karin bayani. *Amsa* To dan'uwa abin da yake sunna shi ne mamu su yi sahu a bayan liman, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisai ingantattu. Saidai idan aka samu cinkoso aka rasa isashshen wurin, to ya halatta mamu ya yi sahu tare da liman, tun da dama yin wancan din sunna ne. Allah ne mafi sani Duba : Majmu'u Fatawaa wa rasa'il Ibnu Uthaimin a lamba ta: 419. Dr. Jamilu zarewa

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 654 · February 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853