Umar shehu zaria

*HAIHUWA A SUNNAH* Darasi na 2 Na *_Sheikh Abdurrazaq Yahya Haifan, Hafizahullah_* *SASHIN AT-TAHNIK:* *MA'ANAR AT-TAHNIK* Ibn Hajar al-Asqalaani ya ce: *_"at-Tahnik shi ne tauna wani abu da kuma saka shi a cikin bakin yaro, da kuma gogawa a jikin saman bakinsa"_*. A duba Fathu al-Baari 9/588. Al-Imam Badrud-Din al-Aini ya ce: *_"A tauna wani abu, kuma a saka shi a cikin bakin yaro, yin haka shi ne an masa at-Tahnik da shi"_*. A duba Umdatu al-Qaari 21/124. Al-Imam ash-Shaukani ya ce: *_"at-Tahnik shi ne (mutum) ya tauna dabino ko makamancinsa, har sai ya zama narkakke, ta yanda za a iya hadiyewa, sannan ya bude bakin jinjiri kuma ya saka shi a cikinsa, domin wani sashi daga ciki ya shiga cikinsa"_*. A duba littafin Nailul audar 5/230. As-San'ani ya ce: *_"at-Tahnik shi ne (mutum) ya saka dabino ko makamancinsa a cikin al-Hanak na jinjiri, har sai wani sashi daga gare shi ya sauka (zuwa) cikinsa"_*. A duba littafin Subulu as-Salam 4/194. Ibn al-Athir ya ce: *_"(Shi ne) a tauna dabino kuma, kuma a goga shi a jikin al-Hanak._* A duba littafin An-Nihaayatu fi Garibi al-Hadith 1/451. Sheikh Albani ya ce: *_"at-Tahnik shi ne: Ka tauna dabino har sai ya yi laushi, sannan ka goga shi a jikin Al-Hanak na yaro"_*. Sahihu al-Kalimi ad-Dayyib 162. Kuma abun da ake nufi da Al-Hanak shi ne: saman baki ta cikinsa. A duba littafin Al-Mu'ujumu al-Wasid 203. Ibn Manzur ya ce: *_"Al-Hanak" a jikin mutum da kuma dabba, shi ne wajen da ya buya ta saman baki, ta ciki"_*. Lisaanu al-Arab 2/632. *ASALIN AT-TAHNIK* At-Tahnik ya samo asali daga Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallam, Al-Bukhari da Abu Dawud, sun riwaito Nana Aisha, Allah Ta'ala Ya yarda da ita, tana cewa: *_"Lallai ne, Annabi, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya kasance ana zuwa masa da yara (jarirai), sai ya musu addu'ar samun albarka, kuma ya musu at-Tahnik!"_* a duba littafin Sahihu al-Jami'i 4876, Sahihu al-Kalimi ad-Dayyib 213, Sahihu Muslim 14/123, Sahihu Al-Bukhari 222, 5468, 6355. Wannan hadisin yana siffanta mana halin Sahabbai, ta sashin girmama Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, da kuma kaunar addu'o'insa, don fatan su samu albarkar Allah Madaukaki a kan rayukansu, da na yaransu. *WADANDA ANNABI YA MUSU AT-TAHNIK:* *JARIRIN AZ-ZUBAIR IBN AL-AWWAAM* Nana Aisha da Asma'u, dukkan su yaran Abubakar as-Siddiq ne. Sun bayar da labari game da haihuwan... Mu hadu a Darasi na 3 in sha Allahu Ta'ala. ✍🏼 Tattarawa: *_Umar Shehu zaria

by: Abdurrahman Bello Yabo · 726 · February 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853