TA YAYA ZAN IYA GANE MUKTARIN SALLAH DA LALURINTA ?

Tambaya: Assalamu alaika mal da Allah amin bayanin yadda ake gàne yanayin muhktari da lalurin sallan Asuba da maghrib? Amsa Wa alaikum assalam, Muktari da laluri, lokuta ne da Allah ya rataya hukunce-hukuncen sallah akan şu, a na gane muktarin sallar asuba idan alfijir na biyu ya keto, ana gane lalurin sallar asuba idan gari ya yi fayau, an gane muktarin sallar azahar idan rana ta karkata daga tsakiyar sama, ana gane lalurin sallar azahar idan inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lokacin la'asar zababbe ya shiga idan inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lalurinta ya shiga idan inuwar mutum ta ninka tsawonsa, ana gane muktarin sallar magriba, idan rana ta fadi, Muktarin sallar Isha yana shiga idan ragowar Jan rana ya buya (shafaki) Bayan dare ya raba lokaci ne na lalurin magriba da Isha. ALLAH NE MAFI SANI Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

by: Mubarak Auwal · 2,052 · January 17, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853