NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI ?

*Tambaya? *Assalamu alaykum Warahmatullahi,* Da fatan malam yana lafiya, Malam ya halatta namiji yayi kunshi? *Amsa: Wa alaikum assalam Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi s.a.w. ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R.A lokacin da ya musulunta ranar bude Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al’ar’na’u’d ya inganta. Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi dazai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la’anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784. Yana daga cikin ka’diojin daya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana sabawa daga al’ada zuwa wata. Allah shine mafi sani Dr. Jamil Yusuf Zarewa* 13/4/1438=11/1/2017

by: Mubarak Auwal · 1,516 · January 17, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853