BANA SHA'AWAR NAMIJI SAM-SAM, ZAN IYA CIGABA DA ZAMA DA MIJINA A WANNAN HALIN?

*Tambaya:* Mata ce da mijinta suke zaune amma kuma matar bata da sha awar namiji ko kadan, ya zamana zaman nasu ya zama mara dadi, tana ganin kamar tana cutar mijinta tunda shi yana da sha awa, shin zamansu ya halatta kuwa a addini? *Amsa:* In har shi ya kan neme ta in sha'awarsa ta tashi, kuma ta biya masa,babu laifi şu ci gaba da zama tare,tun da za ta kare shi daga fadawa cikin haramun, sannan akwai mata da yawa da Allah ya halicce su a wannan yanayin. Zamanku zai iya zama cuta ne in har ya kasance ba kya biya masa bukata ta yadda zai kalli matar da bata hallata a gare shi ba. An shar'anta aure ne saboda samun zuriyya da kuma katange ma'aurata daga zina, kamar yadda ya tabbata a dalilan sharia, duk auren da ya gaza cika wadannan manufofi akwai matsala a cikin shi. Allah ne mafi Sani. Dr jamilu Zarewa.

by: Mubarak Auwal · 3,928 · January 17, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853