ANA YIN WUTIRI NE A KARSHEN DARE

*Tambaya:* Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam menene hukuncin yin wuturi a lokacin taraweeh bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare? *Amsa* Wa alaikum assalam, in har mutum ya san zan yi wata sallar bayan tarawihi, to abin da yake dai dai shi ne ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare saboda hadisin da Bukari da Muslim suka rawaito cewa : Annabi (s.a.w) yana barin wutirin sa in ya yi sallar dare zuwa lokacin sahur, da kuma hadisin da Annabin yake cewa: Ku sanya wutiri sallarku ta karshe da daddare". Bukari ne ya rawaito da Muslim. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu zarewa.

by: Mubarak Auwal · 1,119 · January 17, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853