SADUWA DA MAI HAILA, BAYAN DAUKEWAR JININ, KAFIN TAYI WANKA!!

Tambaya? 5/4/1438=4/1/2017 *Assalamu alaikum,* Malam kasancewar saduwa cikin haila laifi ne, to ina hukuncin saduwa bayan tabbatar da daukewar jinin amma gabanin wankan tsarki?? *Amsa:* *Wa alaikum assalam,* Maganar mafi yawan malamai Shi ne: ba'a saduwa da mai Haila sai ta yi wanka, saboda fadin Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 222 (Idan Mata suka yi tsarki, to ku zo musu ta inda Allah ya umarce ku), inda suka fassara tsarki a wannan ayar da wanka, Kamar yadda Ibnu Rushd ya ambata a littafinsa Bidayatul Mujtahid. Saidai shehin malami Abu-hanifah ya fahimci tsarki a wannan ayar da yankewar Jinin haila, wannan yasa suka halatta saduwa da macen da ta kammala haila kafin ta yi wanka. Duk da cewa duka maganganu biyun suna iya shiga ayar, saidai zance mafi inganci Shi ne maganar farko saboda Allah ya kira haila da kazanta a cikin Alqur'ani, kazanta kuma tana bukatar tsafta da gyaran jiki, don kaucewa bacteriar(kwayar cuta) da ta kunsa. Allah ne mafi sani. Amsawa:✍🏻 *Dr Jamilu Zarewa*

by: Mubarak Auwal · 6,743 · January 05, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853