SHIEKH JA'AFAR SALLAR NAFILA INGANTATTU.

SHEIKH JAFAR SALLAR NAFILOLI INGANTATTU !!! *************** *************** ************** Raka'a 2 kafin sallar Subh Raka'a 4 kafin Zuhr Raka'a 2 bayan Zuhr Raka'a 2 bayan Magrib Raka'a 2 bayan Ishaa Wadannan sune sallolin nafilar da Manxon Allah yake yinsu kuma yace duk wanda ya kiyaye su (wato yana yinsu) za a gina masa gida a gidan aljanna kuma Sahabban sa sukeyi har wasu suka maida ta kamar farilla .. Sanan wadannan sallolin babu wasu surori da ake karantawa se Fatiha da kuma duk wata sura da muka ga sunfi mana sauqi... Amma akwai wasu nafiloli da yazo daga bakin Manxon Allah wanda yake karanta musu wasu surori sune kamar haka : Wato SALATUL FAJR (raka'a 2 kafin Subh), yana karanta Fatiha da Suratul Kafirun a farko, raka'a ta biyu yana karanta Fatiha da suratul Iklass, sanan yace tafi duniya da abunda yake cikinta alheri . Se sallar Shaf'i wal Wutri ita yazo yana yin raka a 11 ko 9, 7, 5, 3, mafi karancinta shine raka'a 1 , amma mafi al ummar sa sun tafi akan yin raka a 3 din ya tabbata yana karanta a farko, : Fatiha da Suratul A'ala (sabbi ismarabbika), rakaa 2 yana karanta fatiha, da Suratul Kafirun. se wutri 1 yana karanta : Fatiha , Iklas, Falaq, Nasi . Yana daga fallalar wana Sallah ..Manxo s.a.w yace duk wanda ya mutu baya yin wanan sallar ranar lahira ze dinga jin kunya mu hadu dashi yana me buya . Se Salatud Duha (walha) ita raka'a 2 yayin da hantsi yayi daga 8am zuwa 11am. Ana karanta surorin d ake karantawa a Raka'atainil Fijr. Tana d falalar ta Annabi s.a.w yace a aljanna akwai wata kofa ana ce mata Babud Duha... Babu me shigarta se wansa yake sallar duha ALLAH Ya bamu ikon yi WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH (S.A.W) Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Waye zai karbi wadannan kalmomi guda 5 daga gareni, ya yi amfani da su ko ya sanar da wanda zai yi amfani da su?" Sai Abu Huraira (r.a) ya ce Ni zan karba ya Ma'aikin Allah. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya riqe hannu na ya maimaita min su sai ya ce; 1. "Ka guji aikata sabo, za ka zamo wanda ya fi kowa bauta a cikin mutane. 2. "Ka yarda da abinda Allah Ya baka, za ka fi kowa arziqi cikin mutane. 3. "Ka kyautatawa maqobcin ka, za ka zamo (cikakken) Mumini. 4. "Ka so wa mutane abinda ka ke so wa kanka, za ka kasance (cikakken) Musulmi. 5. "Ka da ka yawaita dariya , domin yawan Dariya na kashe zuciya. SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA 930. MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE KA RIQE SU KO KA SANAR DA WANDA ZAI YI AMFANI DA SU. IDAN KA TURAWA YAN'UWA MUSULMAI BA KA SAN WA ZAI YI AMFANI DA SU BA, KA GA KA SAMU LADAN MUTANE MASU YAWA. Mafi yawancin mu, muna yin sallar jana'iza, amma kuma bamu san abin da ake fada a Cikin kowace kabbara ba. . Domin fahimtar yadda ake yin sallar janai'za, ainihi dai jana'iza tana da babban lada, ga wanda ya aikata ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar; dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya. . Sallar jana'Iza tana da kabbarori guda hudu ne kawai (4) . KUMA KOWACCE KABBARA, DA ABIN DA AKE FADA A CIKINTA . (1). KABBARA TA FARKO Ana karanta Suratul- Fatiha ne kawai, babu wata sura ko wata Ayah . (.2.) KABBARA TA BIYU Ana karanta Salatin Annabi (SAW) ba wani salati na dabam ba . (.3.) KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu Mace ko Namiji . (4.) KABBARA TA HUDU zaka yi addu'a ne a kanka da sauran al'ummar Musulmi. . DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman yayi sallama . ITA KUMA SALLAMAR Guda daya ce Tak! Kuma zaka yi tane a bangaren daman ka. . Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (SAW). . ALLAH KASA MU CIKA DA IMANI

by: Mai Umar Isa Biu · 10,282 · December 19, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853