ZA MU IYA AURAWA KANWARMU DAN SHI'A?

Tambaya: Assalamu'alaikum da fatan malam yana lafiya.. Malam wata kanwarmuce ta kamu da son dan shi'a dake ungurmu kuma munyi kokarin rabasu saboda wasu daga cikin munanan dabi'ar su kamar zagin sahabbai, mutu'a, zagin matan Annabi da dai sauransu. Amma abin dai ya gagara. Sai dai ya tabbatar mana da cewa shi tinda aka halicce shi bai taba aikata wadan nan laifukan ba. Sannan kuma bai yarda da hakan azuciya ko a baki ba. Illah iyaka yasan yana bin zakzaky ne akan yana kiran hadin kai ga musulmi. Shi iya wannan ne ya amsa amma ya barranta ga duk wani munmunar akidar shi'a. A iya zaman da mukayi dai bamuga yana aikata wani kaba'irar ba dan a masallan mu yake sallah tin tashin mu dashi. Shin malam ya halatta mu bashi. Ko kada mu bashi. Amsa: To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai manyan abubuwa wadanda suke warware musulunci: 1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi da yawa a cikin alqu'ani, duk wanda ya ce mafi yawancin sahabban Annabi (S.A.W) sun kafirta tabbas ya karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a fili yake. 2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa: Alqur'anin da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa: Allah ya tabbatar zai kiyaye shi, har abada. 3. Rafidha 'yan shi'a sun tafi akan cewa Nana A'isha Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita daga abinda munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi guda goma a suratun Nur. Duk da cewa da yawa daga cikin 'yan shi'a suna kore wadannan aqidu, saidai ayyukansu da littatatafansu da maganganunssu, suna karyata korewarsu. Shugabansu Zakzaky yace ba ya zagin sahabbai, kawai sai muka gan shi a zaune a Husainiyyar Zariya yana la'antarsu, Haka Yakubu Yahya na Katsina shi ma ya yi ikrarin haka, sai ga shi mun ji shi yana siffanta Sahabbai da 'yan PDP, yana ci musu mutunci da cewa sun yi juyin mulki. Ya wajaba ka sani yana daga cikin manyan aqidun 'Yan shi'a TAKIYYA wato yin karya ga wanda ba dan shi'a ba, kuma duk wanda bai iya wannan ba, to bai cika dan shi'a ba a wajansu, domin ginshikin addininsu ce, don haka kar ka dogara da maganarsa. Annabi (S.A.W) yana cewa: "Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084, duk wanda addininsa ya kunshi abinda ya gabata, bai halatta a aura masa mace ba, tun da Allah bai yarda da hakan ba, kuma addininsa ba yardajje ba ne, Allah ya ba ta miji nagari wanda ba dan shi'a ba. Allah ne mafi Sani. ‎ Dr. Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 2,899 · October 20, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853