NA AURI AMARE BIYU A RANA DAYA, YAYA YA KAMATA NA YI WAJAN TAREWA ?

Tambaya : Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya auri mata biyu (sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga? Nagode Allah ya karawa malam imani. Amsa : To dan'uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auran mata biyu a yini daya, saboda hakan zai kawo matsala wajan bawa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara da ita, to dayar za ta cutu, saidai idan hakan ta faru, to zai fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, in kuma sun shigo tare ne sai ya yi musu kuria. Don neman Karin bayani duba : Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na : 981. Allah ne ma fi sani Jamilu zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 4,728 · October 05, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853