HUKUNCIN SHUGABANTAR DA MACE A MUSULUNCI

Tambaya : Salam. Mal Don Allah minene fatawar malamai magabata akan shugabancin mata, kuma zan so ayi post mai zaman kansa akan wannann matsala. Allah ya taimaka. Amsa : Wa alaikum assalam Yawanci malamai magabata suna tafiya ne akan hadisin Abu-bakrah inda Annabi s.a.w. yake cewa ; "Duk mutanen da suka sanya mace ta zama shugabarsu, to ba za su rabauta ba" kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 4425. Don haka bai halatta ta rike shugabanci ba in ba na gidanta ba. Sannan malamai sun ce daga cikin hikimomin hakan shi ne : saboda raunin mace, da tawayar hankalinta, da kuma yawan tausayinta, sannan idan tana haila halayanta sukan canza, ka ga za ta iya yiwa mutane danyen hukunci. Ibnu Khudama yana cewa : " Annabi s.a.w. bai taba sanya wata mace a matsayin shugaba ba, haka nan halifofinsa shiryayyu".Mugni 13\14 Duk lokacin da mutane suka dorawa mace shugabanci lamura za su tabarbare, kuma hakan har lahirarsu sai ya shafa, Shaukani yana cewa : "Babu wani narko da ya fi kore rabauta" Sailul jarrar 4\273 Allah ne ma fi sani Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 1,549 · September 24, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853