ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBAR LAYYA?

Assalamu alaikum mallam dan Allah inason sanin addu'ar da akd yi lokacin yanka dabbar layya. Nagode. AMSA: Addu'ar da ake yi yayin yanka dabbar layya itace. Bayan mai yankan ya dora kafarsa akan wuyan dabbar sai yace: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ‏. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني . Idan kuma zai hada layyar da iyalansa Sai yace: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ‏. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني و آل بيتي Idan kuma wani ne ya waqilta mai yankar ya yanka masa dabbar sai yace: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ( ﻋﻦ ﻓﻼﻥ ‏) ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻦ (ﻓﻼﻥ) ﻭﺁﻝ (ﻓﻼﻥ) ‏ A duk inda aka ga an saka wannan fulaan (فلان) din sai a kira sunan mai layyar. "Fulaan" yana nufin "WANE" TARJAMA Bismillaah, wa Allaahu akbar, Allaahumma haaza minka wa laka, haaza ‘anni. Allaahumma taqabbal minni wa aali baiti. Ko kuma a maimakon cewa Allaahumma taqabbal minni wa aali baiti. Mutum yana iya ambatar sunansa wato misali idan sunansa Usman sai yace Allaahumma taqabbal min Usman wa aali Usman Kamar yanda Annabi (sallallahu alaihi wasallam ya ambaci sunansa da iyalansa da kuma al'ummarsa. Idan kuma wani ne ya waqilta mai yankar ya yanka masa sai yace: Bismillaah, wa Allaahu akbar, Allaahumma haaza minka wa laka, haaza ‘an [ fulaan], Allaahumma taqabbal min [fulaan] wa aali [sai kira sunan mai layyar]. Amma fa abin lura anan shine cewa BISMILLAAH kadai ne wajibi. Sauran duk mustahabbi ne ba dole bane. Domin qarin bayani: Al- Bukhaari (5565), Muslim (1966), Muslim (1967), Al-Tirmizi (1521), Sharhul Mumti (7/492). Wallahu a'alam سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

by: Mubarak Auwal · 7,277 · September 09, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853