SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?

Tambaya : salam malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka menene hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma wai don Allah ka amsa a face book, saboda ana bukatar sanin amsar. Amsa : To 'yar'uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba'a samu magabata na kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba'a yin ta sai da dalili daga Alqur'ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake yiwa kansa dawafi. Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, saidai ba'a samu na dawafi a karan kansa ba. Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka hada jiki da dukiya, duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah. ALLAH NE MAFI SANI Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta : 87 Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 929 · September 07, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853