'YAMMATAN DAJIN SAMBINSA, ZA'A IYA ZUBAR DA CIKIN DA SUKA DAUKO ?

Tambaya : Don Allah Shehi me za Ku ce game da yanayin mata masu ciki ta hanyar fyaden Yan Boko Haram, wadanda aka Kwato su a Sambisa. MUNA bukatar nusarwa a shariance game da me za a yi da cikkunansu. A zubar Ko a Bari.? Idan za mu samu amsa a mafi kusancin lokaci za mu so haka.. Na gode. Amsa : To dan'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu : 1. Idan ya zama cikin na zina ba'a busa masa rai ba, kamar ya zama bai kai kwanaki 120 ba, to wannan malamai sun yi sabani akansa zuwa maganganu uku : A. Wadanda suka tafi akan halaccin zubar da shi, saboda bai zama mutum ba, kuma in an haife shi zai zama aibi ga uwarsa, shi ma kuma ba zai yi rayuwa mai dadi ba. B. Bai halatta a zubar ba, saboda Annabi s.aw. bai umarci Gamidiyya da ta yi zina ba, ta zubar da cikinta, cewa ya yi da ita : ta je ta haife, sai ta zo a tsayar mata da haddi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1696. C. Akwai malaman da suka tafi cewa : idan fyade aka mata, za'a iya zubarwa, mutukar ba'a busa rai ba. 2. Idan ya zama bayan an busa masa rai, wannan kam bai halatta a zubar ba, saboda kashe rai ne, wanda bai ji ba bai gani ba, yana daga cikin manufofin sharia kiyaye rayuwar dan'adam . Zance mafi inganci shi ne bai halatta a zubar da cikin zina ba ko da ba'a busa masa rai ba, saboda hakan zai iya bude hanyar yaiwaita zinace-zinace, tun da za'a iya zubar da cikin ba tare da an shiga cikin kunci da kunyata ba, amma idan Fyade aka yi mata, ko kuma likita ya tabbatar da cewa za ta halakka idan ta cigaba da zama da cikin, to ya halatta a zubar a irin wannan lokacin . Mutukar an busawa ciki rai bai halatta a zubar ba, ko da kuwa fyade ne . Don neman Karin bayani duba Ahkamul-janin Fil-fiqhil Islamy na Umar Ganam Allah ne mafi sani . Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 3,099 · September 03, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853