AZUMI GOMA A FARKON ZUL-HIJJA ?

Tambaya: Assalam alaikum Dan Allah mlm menene ingancin azumi Guda goma da ake awatan zulhijja? Amsa: Wa alaikum assalam, Hadisi ya tabbata a Sunan Annasa'i: Annabi (s.a.w) ya kasan ce yana azumtar kwanaki Tara na farkon Zul-hijja. Ba'a azumtar rana ta goma saboda ita ce ranar sallah, Annabi (s.a.w) ya haramta azumtar ranar sallah a hadisin da babban sahabi Umar ya rawaito. Allah ne mafi sani Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.

by: Muhammad Basheer Ridwan · 1,259 · September 03, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853