ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

Tambaya : Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci Amsa : To dan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa : suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka : 1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su . 2. Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci. 3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa. 4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta 28 5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci. 6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya. 7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida. 8. Barin baccin da ba shi da amfani. 9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka. 10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata. Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci. Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22 Allah ne ma fi sani ***Dr. Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 4,861 · August 28, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853