YA WAJABA CANJI YA ZAMA HANNU DA HANNU

Tambaya: Me ne ne matsayin kasuwancin da muke yi, zamu karbi dalar mutum bayan mun daidaita farashi, amma ba zamu bashi kudi ba har sai mun je mun sayar wa da namu customan kuma mun dora namu riban kuma mu zare ribar mu, sannan mu kawo wa mai dala kudin sa a kan farashin da muka daidaita da shi? Amsa : To dan'uwa wannan nau'i na canji bai halatta ba a musulunci, saboda yana daga çıkın sharudan canji ya zama hannu-da-hannu, tsakanin abin da za'a canza da wanda za'a canzar, kamar yadda hadisin Ubadah mai lamba ta : 2978 a sahihi Müslim yake nuni zuwa hakan. Don haka bai halatta ka amshi dalar mutum ba, in har ka san ba ka da nairar da za ka ba shi a lokacin, Bin shari'ar Allah yana sanya albarka a Kasuwanci. Allah ne mafi sani Dr. Jamilu Zarewa 13\12\2015

by: Mubarak Auwal · 681 · August 25, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853