AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI ?

Tambaya : Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci. Malam matsala ta haihuwa greni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na nkeyi nacigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin tawa take. Amsa: To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a cikin alqur'ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah da azumi ba. Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al'ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa. Allah ne mafi sa ni DR, Jamilu Yusuf Zarewa

by: Mubarak Auwal · 1,223 · August 25, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853