ZAN IYA YIWA BUDURWA SALLAMA ?

Tambaya: DR barka da assubah, malam maye hukuncin yima mata sallama a lokacin da ake kiliya da su a kan hanya?, 'yan mata da kuma na aure wanda na sani da wanda ban san su ba, sai bayan na musu sai kuma naji duk na tsargi kaina. bissalam Amsa: Wa alaikum assalam, An tambayi Imamu Malik game da yin sallama ga mata, sai ya ce: Game da budurwa bana son hakan, Amma game da tsohuwa,to Ba zan hana hakan ba, kamar yadda ya zo a Muwaddah. Wannan shi ne mazhabar mafi yawan malamai. Ya halatta ka yiwa maharramarka sallama ko matar da ka tabbatar ba za ku fitunu da juna ba. Ya halatta ga namiji ya yiwa taron mata sallama, lokacin da suke da yawa,saboda hadisin Abu-dawud: Annabi (S.a.w) wuce taron wasu mata sai ya yi musu sallama. Allah ne mafi sani Dr Jamilu Zarewa.

by: Muhammad Basheer Ridwan · 1,648 · August 20, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853