BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?

Tambaya? Assalamu Alaikum. Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci? Amsa: Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo. Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo". Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida suka siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri. Allah Ne mafi Sani. Dr Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 512 · August 16, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853