KUBUTA DAGA FITINTINU DA KALLON HARAM

Duk wanda yake son ya kubuta daga shaukin mata da kuma da kallon haram, to ya nemi taimakon Allah, sannan ya dawwama akan salloli guda biyar,domin ita sallah tana hana alfasha da mummunan aiki, sannan kuma kar ya manta da addu'a da Kankan da kai a lokutan amsar addu'a ga Allah madaukaki, ( kamar lokacin sahur da tsakanin kiran sallah da ikama da cikin sujjada) ya dinga yawaita cewa : Ya mai jujjuya zukata ka tabbatar da ni akan addininka. Ya kuma yi kokari wajan nisantar wuraren fitina ta hanyar canza su da halal mai tsarki, ya dinga tuna fadin Annabi s.a.w. cewa : (Duk wanda ya bar abu saboda Allah, to Allah zai canza masa da abin da ya fi shi alkairi) Ibnu Mas'ud yana Mas'ud yana cewa : "Idan wata mace ta birge dayanku, to ya tuna kazantarta (fits arinta da bahayarta)" saboda zai taimaka ya kau da ido daga kallonta. Dr. Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 2,243 · August 04, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853