AZUMIN NAFILA RANAR ASABAR !

Tambaya : Dr maganar azumi wani malami yace : indai kamata ne mutum yayi Alhamis da Juma'a, don anyi hani da yin azumi ran sati ? Amsa : To 'yar'uwa hadisi ya zo daga Annabi s.a.w cewa : "Kada ku yi azumi ranar asabar sai abin da aka farlanta muku" Abu-dawud hadisi mai lamba ta :2423. Saidai malamai sun yi sabani akan ingancin wannan hadisin, akwai malaman da suka tafi akan cewa hadisin karya ne, Abu-dawud ya hakaito hakan daga Imamu Malik. Akwai wadanda suka ce hadisin akwai kuskure a ciki, saboda ya sabawa hadisin da ya fi shi inganci, inda Annabi yake cewa : "kada dayanku ya azumci ranar juma'a, sai in ya azumci yinin da yake gabaninta, ko kuma wanda yake bayanta" Bukhari a hadisi mai lamba ta : 1884, wannan hadisin yana nuna halaccin azumtar asabar ga wanda ya azumci juma'a. Akwai malaman da suka tafi akan cewa hadisin ya inganta saidai an goge shi da wasu hadisan, saboda yadda aka rawaito cewa annabi yana azumtar mafi yawan Sha'aban, wannan sai ya nuna cewa dole asabar ta fado a cikin azuminsa, ga shi kuma Annabi s.a.w. ya halatta irin azumin Annabi Dawud, wanda za ka yi azumi yau ka sha gobe, babu yadda za'a yi mutum ya yi azumin Annabi Dawud ba tare da Asabar ta fado a cikin azuminsa ba. Zancen miliyoyin malamai shi ne ya halatta ayi azumi ranar asabar ga wanda ya yi azumi ranar juma'a. Don neman karin bayani duba: Tahzibu sunani Abidawud 1\469 Allah ne mafi sani Jamilu Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 2,125 · July 23, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853