IDAN DREBA YA KASHE MUTANE BAKWAI, YAYA KAFFARARSA ?

Tambaya: Assalamu alaykum tambayata anan shine idan tsautsayi yasa Kai ajalin rai bakwai da motarka, idan zakai axumi na kaffara nawa zakai ? Amsa: To dan'uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu: 1- Diyya wace dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe. 2- Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi :60, kamar yadda aya ta 92 a Suratunnisa'i take nuni zuwa hakan. Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga Driban motar ya yiwa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarta ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Driba, ko wuce ka'idarsa. Idan hadari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Driba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yiwa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hadarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dai dai da abun Allah ne mafi sani. Don neman Karin bayani duba : Al'inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352. Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

by: Muhammad Basheer Ridwan · 1,747 · July 21, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853