IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44, IDDARTA TA CIKA ?

Tambaya: السلام عليكم ورحمة الله Malalm don Allah a taimakamin da amsar wannan tambayar: Mace ce mijinta ya rasu ya barta da ciki wata daya, bayan sati 2 da rasuwarshi sai cikin yazube to anan ya iddarta take? 1. iddar ta kare? 2. ko zata kirga wata 4 da kwana 10? in kuma kirgar zat ai daga yaushe zata fara, ranar rasuwarshi ko ranar da cikin ya zube? na gode. Amsa: Wa alaikum assalam, Mutukar cikin na ta bai wuce kwana : 44 ba, ba za ta kammala iddar takaba da yin barinsa ba, tun da halittar mutum ba ta fara bayyana ga dan-tayin ba. Mafi karancin lokacin da halittar mutum take fara bayyana yana farawa ne daga kwana: 80 zuwa 90. Idan haka ta faru da ita za ta yi idda da wata hudu da kwana goma. Allah ne mafi sani.d Dr Jamilu Zarewa.

by: Muhammad Basheer Ridwan · 1,190 · July 20, 2016

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853